1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure sun mutu a turmitsitsi

Ramatu Garba Baba
June 25, 2022

Bakin haure da suka fito daga kasashen Afirka akalla 18 ne suka mutu a turmutsitsi yayin tsallaka wani shinge don shiga kasar Spain

https://p.dw.com/p/4DEEL
Migranten in der spanischen Nordafrika-Exklave Melilla
Hoto: Javier Bernardo/AP/dpa/picture alliance

Wasu bakin haure da suka fito daga sassa dabam-daban na Afirka guda goma sha takwas, aka tabbatar sun mutu a yayin wani turmutsitsin tsallaka shinge da ya raba kasar Moroko da kasar Spaniya a ranar Juma'ar da ta gabata.

Bakin haure sama da dubu biyu ne suka yi yunkurin haura katangar shingen, wasu sun fado daga saman shingen da ya raba kasashen biyu, akwai  jami'an tsaro kimanin dari da arba'in da kuma bakin haure saba'in da shida da suka ji rauni a yayin yunkurin tsallakawa. 

An kafa katangar a mashigin tekun Melilla na kasar Spaniya, don hana bakin haure tuttudowa Turai daga Moroko, sai dai ya kasance tamkar tarkon mutuwa ganin yadda ake ci gaba da tafka asarar rayuka a saboda yadda bakin haure ke kasadar shiga Turan duk da barazanar rasa rai.