Bakin haure na ci gaba da shiga hadari | Labarai | DW | 16.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bakin haure na ci gaba da shiga hadari

Rayuwar bakin haure dake fatan zuwa Turai a kullum sai dada shiga garari take, sakamakon hadarin da suke fuskanta a tekun Medeterranean.

Kimanin bakin haure 75 ne suka tsallake rijiya da baya a ranar Laraba, bayan da dakarun sojin kasar Malta suka ceto su yayin da jirgin dake dauke da su ya kusa nutsewa sakamakon karfin igiyar ruwa da kuma iska mai karfin gaske a teku.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan al'amari dai na zuwa ne a dai dai lokacin da Firaministan kasar ta Malta Joseph Muscat, ke yin kira ga kasashen nahiyar Turai su dauki kwararan matakai domin magance matsalar bakin haure da a kullum ke yin tururuwa a yunkurin da suke na shigowa Turan, yana mai cewa ya kamata su aiwatar da matakan da suka ce za su dauka.

Daruruwan bakin haure ne dai suka rasa rayukansu a wannan wata da muke ciki a tagwayen bala'oin hadarin jiragen ruwa da suka faru. Inda na farko ya afku a ranar 3 ga wannan wata a kusa da Tsibirin Lampedusa na kasar Italiya, yayin da na biyun ya afku a ranar 11 ga watan na Oktoba da muke ciki tsakanin Tsibirin na Lampedusa da kasar Malta.

Mawallafiya:Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammed Nasiru Awal