1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar bakin haure daga Afirka a teku

Binta Aliyu Zurmi
August 31, 2021

Kimanin bakin haure daga kasashen Afirka 30 ne ake fargabar sun rasa rayukansu, a yayin da suke kokarin tsallaka wa kasashen Turai ta gabar tekun kasar Spain.

https://p.dw.com/p/3zjaI
Weltspiegel 20.05.2021 | Spanien Ceuta Abschiebungen
Hoto: JON NAZCA/REUTERS

Masu aikin ceto a teku dai, sun yi nasarar ceto wasu daga cikin mutanen da ke makare a cikin wani jirgin ruwa. Wadanda aka ceto sun ce jirgin ya dauko sama da mutane 60, amma su 32 ne suka samu damar tsira da rayukansu. Bakin haure dai na amfani da wannan barauniyar hanya wajen shiga Turai, abin kuma da ke ci gaba da lakume rayukan mutane manya da yara amma har ya zuwa wannan lokaci an kasa kawo karshen matsanancin halin da mutane ke jefa kansu a ciki.