Baki na ci gaba da kaurace wa Afrika ta Kudu | Labarai | DW | 20.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Baki na ci gaba da kaurace wa Afrika ta Kudu

Kisan baƙin na ƙasar Afirka ta Kudu guda bakwai cikin wannan wata ya jawo fushi da ma yin tofin Allah tsine a faɗin nahiyar.

Sakamakon rashin tabbas na lafiya da rayukan al'umma ɗaruruwan baƙi da ke ci rani a ƙasar Afrika ta Kudu na ficewa daga ƙasar cikin motoci kirar bus a yau Litinin bayan kai farmaki a shagunan baƘi da ke a Ƙasar.Kisan baƘin na Ƙasar AfIRka ta Kudu guda bakwai cikin wannan wata ya jawo fUshi da ma yin tofin Allah tsine a faɗin nahiyar. Aƙalla jami'an diplomasiya biyu sun bayyana wa ƙasar ta Afirka ta Kudu a ƙasashen da suke zaune cewar akwai fargaba ta yin ramuwar gayya kan 'yan ƙasashen da ma dukiyoyinsu.

Wannan tashin hankali dai na ƙara zubar da kima ta wannan ƙasa wacce ta yi suna da samun ci gaba na tattalin arziki da kan sanya baki daga wajen ƙasar sha'awar zuwa dan neman ingantacciyar rayuwa.