Baki da dama sun halaka a harin Tunisiya | Labarai | DW | 26.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Baki da dama sun halaka a harin Tunisiya

A kwai mutane daga kasashen waje da ke wasanni a farfajiyar otel din da wadanda ke yin linkaya a cikin ruwa da aka tanada ga masu sha'awa.

Mutane sama da ashirin ne suka rasu bayan da wani dan bindiga dadi ya kai hari a wani otel a garin Sousse da ke samun baki daga kasashen waje a Tunisiya. Mai magana da yawun ma'aktar harkokin cikin gidan kasar ta Tunisiya ya bayyana haka a ranar Juma'an nan.

A cewar Mohamed Ali Aroui da ke magana da yawun ma'aikatar harkokin cikin gidan Tunisiya ya ce wannan hari dai an kai shi ne a wani otel da ake kira Marhaba da 'yan yawon bude ido ke sauka a cikinsa idan sun isa kasar ta Tunisiya.

A kwai mutane daga kasashen waje da ke wasanni a farfajiyar otel din hada da yin linkaya a cikin ruwa da aka tanada ga masu sha'awa. Har yanzu dai ba a bayyana kasashen da mamatan su ka fito ba.