Baje kolin fasahar Kwango na shekaru 50
Birnin Tübingen na Jamus ya dauki bakuncin nuna ayyukan fasaha da 'yan Kwango suka samar tun daga shekarun 1960. Har zuwa karshen watan Yuni, baki za su ga abubuwan ban mamaki da aka samar a wuraren da dama na Kwango.
Hoton wadata da fata na gari na Kwango
Bisa zane mai taken "siffar arziki da kuma kyakkyawar Kwango" mai aikin zanen fasaha Makenge Mamungwa da aka fi sani da suna SAPINart, ya nuna kyakkyawar makoma da ya ke so kasarsa ta samu. Ko da yake Jamhuriyar Dimukiradiyyar Kwango na da arzikin albarkatun karkashin kasa, amma ta kasance daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya. Amma zanen ya nuna cewa tana da ci gaba sosai.
Maci na goyon bayan yaki da HIV/AIDS
Cheri Samba yana daya daga cikin taurarin masu zane-zane na kasar Kwango. Ya kafa makarantar aikin fasaha ta "Zaire School of Fine Painting" a Kinshasa, kuma ya wakilci kasarsa a bukukuwan nune-nunen fasaha a duniya tun 1989. A cikin zane-zanensa yana nuna rayuwar yau da kullum ta Kwango - ciki har da labaran da suka shafi kida da waka da talauci da cututtuka irin su AIDS/SIDA.
Sashe na 15 na kundin tsarin muki
Bayangu Mayala, wanda aka fi sani da suna Maître SYMS, ya koyi aikin zane a makarantar fasaha ta Cheri Samba kafin ya bude ta kansa a shekarar 1977. Ya sadaukar da aikinsa kan batutuwan da suka shafi damuwa ta yau da kullum a Kwango. A cikin aikinsa mai taken "Mataki na 15" ya yi amfani da Sashe na 15 na Kundin tsarin mulki kasar Kwango wajen nuna cewa dole kowa ya kula da kansu.
Nganda Tika Muana a shekarar 1992
Monsengo Kejwamfi, da aka sani da suna "Moke" ya koyi zane da kansa. A yau shi ne daya daga cikin manyan masu fasaha na kasar Kwango. Yana daukar kansa a matsayin "dan jarida mai zane-zane". Yawancin ayyukansa na nuna tabarbarewar zamantakewa a Kinshasa, inda aka fi dogara kan kudi da masha'a sabanin yadda lamarin ya gudana a baya.
Tauraron dan Adam mai suna Sarki
Monsengo Shula ya fara zane-zane a jikin bango a matsayin mai taimaka wa dan uwansa Moke yana da shekaru goma sha biyar. "Roi satellite" yana nufin kwarya-kwaryar shirin sararin samaniya da Zaire ta fara a zamanin mulkin Mobutu a cikin shekarun 1970. Kaloli dabam-daban na "Afronauts", da ke haduwa a cikin sararin samaniya na nuna alamar ci gaba da wadata.
Mafarkin balagoro da jirgin kasa
Bisa dogaro kan aikin zanen mahaifinta, Gosette Lubondo ta sadaukar da kanta wajen daukar hotuna yayin da ta ci gaba da karatun zane-zane a wata makarantar koyan aikin fasaha ta Kinshasa. A cikin jerin hotunanta na '' Mafarkin tafiya '' ta yi tsokaci game da bukatar tafiye-tafiye (ta hanyar jirgin kasa), wanda ya kasance da kamar wuya a Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango saboda rashin layin dogo..
Zaben manyan mutane cikin barkwanci
Joseph Kinkonda, (Cheri Cherin), ya yi karatu a "Académie des Beaux-Arts na Kinshasa". Daga cikin malamansa har da dan kasar Austiriya Peter Weihs. A shekarun 1970 ya yi zane a "fannin al'adu", wanda ke zama na fitattun mutane da wadanda aka mayar saniyar ware. Masu zane-zane kamar Cheri Cherin suna amfani da barkwanci wajen nuna matsaloli da Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango ke fuskanta.
Komabaya a fannin al'adun Kwango
Eddy Kamuanga Ilunga ya kafa studio "M'Pongo" tare da masu fasahar zane-zane da dama a shekara ta 2011. A cikin jerin zane-zane mai taken "Rashin Makoma" ya yi la'akari da bayan samun 'yancin kai, inda al'adu da tattalin arziki suka ja baya sakamakon amfani da injuna. Ayyukansa da na sauran masu fasaha na daga cikin wadanda za a nuna a birnin Tübingen har zuwa karshen Yuni.