1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mali: Shugaban rikon kwarya yayi murabus

Ramatu Garba Baba
May 26, 2021

Shugaban rikon kwarya Bah Ndaw da Firaiminista Moctar Ouane sun sanar da yin murabus a yayin zaman sulhunta rikicin da Kungiyar ECOWAS ta shirya.

https://p.dw.com/p/3tzN8
Mali | Interimspräsident Bah Ndaw
Hoto: Amadou Keita/Reuters

Shugaban gwamnatin rikon kwarya a Mali Bah Ndaw da Firaiminista Moctar Ouane, sun sanar da yin murabus a wannan Laraba, bayan da suka shafe kwanaki biyu a tsare a hannun sojoji a barikin Kati da ke wajen Bamako babban birnin kasar. Sanarwar yin murabus na zuwa ne, jim kadan da soma tattaunawa da aka shirya da zummar kwantar da wutar rikici mai nasaba da jayayya kan shugabancin kasar. Ana ganin matakin na yarda kwallon mangwaro don a huta da kuda, zai taimaka a samar da hanyar kafa sabuwar gwamnati.

Manzo na musamman na Kungiyar ECOWAS kan rikicin Mali kuma tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, shi ya jagoranci zaman don tattauna rikicin da ya sake barkewa. Kasashen Ecowas da Faransa na ci gaba da yi wa sojan kasar da aka ce sun kuma yin wani juyin mulkin, matsin lamba, tare da barazanar daukar mataki na ladabtarwa. A watan Augustan bara sojoji suka kwace iko daga hannun Shugaba Ibrahim Boubacar Keita bisa zarginsa da gazawa a shawo kan matsalar rashin tsaro da Mali ta sami kanta a sakamakon aiyukan 'yan ta'adda.