Badawi ya samu lambar yabo daga DW | Labarai | DW | 25.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Badawi ya samu lambar yabo daga DW

Tashar Deutsche Welle ta bai wa Raif Badawi dan asalin kasar Saudiya lambar yabo kan 'yancin fadin albarkacin baki

Tashar Deutsche Welle ta bai wa Raif Badawi dan kasar Saudiya mai rubutu a shafukan Internet lambar yabo kan fadin albarkacin baki. Badawi da yanzu haka yake tsare ya zama mutum na farko da ya samu wanna lamba ta yabo daga tashar ta DW.

Shugaban tashar ta DW, Peter Limbourg, ya ce daukacin mambobin gudanarwa ta tashar suka amince da ba da lambar kyautar, saboda yadda Badawi ya nuna jajircewa wajen aiki domin tabbatar da fadin albarkacin baki a kasar ta Saudiya, kuma tashar ta yi fatar ganin an saki Badawi da yanzu haka yake gidan fursuna.

Hukumomin kasar ta Saudiya sun cafke Raif Badawi dan shekaru 31 da haihuwa cikin watan Mayu na shekarar da ta gabata ta 2014, inda aka yanke masa hukuncin bulala 1,000, da daurin shekaru 10 gami da tara mai yawa. An yi masa bulala 50 daga ciki a watan Janairu. Tuni matar Badawi mai suna Ensaf Haidar ta yaba da karamcin na tashar Deutsche Welle.