Badakalar mai ta jawo kace-nace a Ghana | Siyasa | DW | 05.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Badakalar mai ta jawo kace-nace a Ghana

Ministan kula da harkokin makamashi a kasar Ghana ya rusa wani kwamitin da ke kunshe da mambobin majalisa takwas da aka kafa don binciken wasu jami'an gwamnatin kasar da ake zargi da almundahana.

GOIL staatliche Ölgesellschaft Ghana Oil Company Limited (Stefanie Duckstein)

Ministan kula da makamashin kasar Boakye ne ya sanar da rusa kwamitin bayan da ya ce hukumar bincike ta kasa BNI da kuma hukumar tsaro duk sun wanke Manajan kamfanin man Alfred Obeing Boateng daga zargin da ake masa na hannu a kan badakalar gurbata mai da gangan a ma'aikatar man kasar.

Ana dai ci gaba da cece-kuce kan wannan mataki da ministan ya dauka, wani abu da ya daure wa al'umma da dama kai, shi ne ko mai ya sa ministan ya riga malam masallaci ganin yadda ya yi saurin yanke hukunci na rusa kwamitin don tsayara daina binciken, Dan majalisa Hon  Dakora ya yi bayani da cewa

‘‘Ga shi a zahiri cewa shugaban kamfanin  ya aikata ba daidai ba, mene ne Ministan ke yin  rufa- rufa, wannan hanya ce ta kauce wa shari'a daga cin hanci da aka aikata, kamata  ya yi a bar kwamitin da aka kafa ta yi aikinta ta kuma fito da sakamakon binciken, ga dai gwamnati mai ikrarin kawar da cin hanci, wannan mataki ya kara jadada kalamun da ya fito daga bakin dan jam'iyyarsu Kennedy Agyapong  da ya ce idan aka salammi shugaban, to zai tona asirin yadda jam‘iyyar  ta ci zaben shekarar 2016‘‘

Ghana Präsident Nana Addo Dankwa Akufo Addo (picture-alliance/Photoshot)

Badakalar mai ya kunno kai a zamanin mulkin Akufo Addo

A daya bangaren kuwa akwai wasu da ke ganin ya kamata shugaban kamfanin ya ja da baya don bai wa hukumomi damar gudanar da bincike, Mr Mensah na jam'iyyar  NPP  shima dai ya bayyana ra'ayinsa yana mai cewa

‘‘Menene dalilin da ya sa zai ja da baya a gudanar da bincike a kan man fetur da aka gurbata, ai harkoki  na cikin gida da tsarin aikin ma'aikata na masu bincike ne ba wai na shugaba ba, Ya aka yi aka gurbata man fetur‘‘

A halin yanzu dai za a iya cewa hankula sun fi karkata zuwa ga yanda  gwamnatin Nana Addo za ta fidda kanta daga cikin wannan badakalar man fetur da kuma zargin yin sama da fadi da kudin kasar Miliyan 7.

Ana dai zargin shugaban kamfanin man da wasu na kusa da shi da gurbata man kamfanin da gangan da sayar da shi da rahusa da zummar cin kazamar riba.

 

Sauti da bidiyo akan labarin