Badakalar kisan yara a Ostareliya | Labarai | DW | 20.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Badakalar kisan yara a Ostareliya

An kama wata mata a kasar Ostareliya saboda kisan wasu yara takwas, bakwai daga cikinsu 'ya'yan da ta haifa kamar yadda 'yan sanda suka bayyana a yau Asabar.

Ana tsare da matar nan 'yar Ostareliya kan mutuwar yara takwas, wadanda bakwai daga cikinsu suka kasance 'ya'yan matar daya kuma 'yar riko.

Matar mai shekaru 37 wacce ke samun sauki a gadon asibiti saboda raunuka da ta samu a jikinta, 'yan sanda na mata tambayoyi tare da sanya idanu a kanta kamar yadda Bruno Asnicar sifeton 'yan sanda a Queensland ya bayyana.

Ko da yake a cewar Asnicar ba a kai ga cajin matar ba, amma 'yan sanda na gudanar da bincike dan sun gano wukake da dama a gidan wadanda suke ganin anyi amfani da su wajen kisan yaran

Yaran dai maza hudu ne mata hudu kuma suna tsakanin shekaru biyu zuwa goma sha hudu. Bakwai 'ya'yan matar yayin da daya ta kasance 'yar 'yan uwanta. Dukkanin yaran dai an ga gawarwakinsu ne a gidan matar.