1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bada na goro don samun aiki a Najeriya.

Usman ShehuJanuary 17, 2013

Majalisar dattawan Najeriya ta fara binciken matsalar cin hanci, wajen ɗaukar ma'aikata.

https://p.dw.com/p/17MZJ
LAGOS, NIGERIA - JULY 15: A detail of some Nigerian Naira,(NGN) being counted in an exchange office on July 15, 2008 in Lagos, Nigeria. (Photo by Dan Kitwood/Getty Images)
Hoto: Getty Images

Sannu a hankali dai ya zamo sabon wuri na tatsa akai gida ga manyan ma'aikatan ma'aikatu da hukumomin gwamnatocin Tarrayyar Najeriya da suka zauna suka rika karba daga hannun masu neman shiga cikin aikin gwamnatin kasar.

An kai ga ritayar dole ga babbar jami'ar hukumar shige da ficen kasar, an kuma kai ga yin gargadi ga kananan dake karkashin ta, duk dai da sunan samar da aikin yi ga aikin dake kanshi irin na dan goma da kuma yanzu haka ya jawo fushin yayan majalisar dattawan Najeriya dake fadar da biyu.

national assembly.jpg
Majalisar dokokin NajeriyaHoto: DW

Majalisar dai ta kafa wani kwamitin da ta dorawa alhakin binciken yanda ake karbar daga naira dubu 200 ya zuwa har miliyan daya domin daukar kananan ma'aikata abun kuma da a cewar senata Ahmed Lawal dake zaman dan majailasar dattawan kasar daga yobe ke zaman babbar barazana ga makomar kasar ta Najeriya. Inda yace hakan zai iya haddasa bore.

Bore ga kasa Najeriya ko kuma neman kudi da sunan aiki dai duk da dokokin kasar ta Najeriya sun tanadi dai daiton ma'aikata a ma'aikatu da hukumomin gwamanti, hukumar da gwamnatin ta kafa dai ya zuwa yanzu na zaman magen lami bata iya cizo balle yakushin masu aikata laifin cin mutuncin ma'aikata.

Eagle Square.jpg
Skatariyar gwamnatin TarayyaHoto: DW

To sai dai  kuma a cewar senata Abdulmumini Hassan dake zaman tsohon jami'in hukumar kuma daya daga cikin masu neman kawo sauyin majalisar matsalar ba ta ga kasawar hukumar.

Batun na son zuciya cikin aikin gwamnati game kuma da halin berar da ya yi katutu a zukatan ma'aikatan ne dai ake ta allakawa da rushewar aikin dama satar da ke zaman ruwan dare gama duniyar kasar ta Najeriya.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Usman Shehu Usman