1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Badaƙƙala game da sha'anin man fetur a Najeriya

January 31, 2013

'Yan Niger Delta na bayyana ra'ayoyinsu game da hukuncin da wata kotun Holland ta yanke akan zargin gurɓata muhalli da ake yiwa kamfanin man fetur na Shell.

https://p.dw.com/p/17VSz
Umweltschäden durch Ölförderung (Shell) im Nigerdelta. Foto: DW/Muhammad Bello, Haussa Korrespondent from Niger Delta( Nigeria), 15.11.2011
Hoto: DW/M. Bello

Wata kotu a kasar Holland ta yake hukunci a tsakanin wasu manoma huɗu 'yan yankin Niger Delta da kuma kamfanin man fetur na Shell da ke aikinsa a yankin na Neija Delta, a wata bukata da manoman suka gabatarwa da kotun cewar kamfanin na Shell ya gurbata musu yanayi da muhalli, kuma suna neman diyya.

Tun dai a shekara ta 2008 ne wasu manoma 4 tare da goyon bayan kungiyar kare muhalli ta Friends of the Earth suka kai karar kamfanin man Shell a gaban wata kotu da ke Hague a kasar Netherlands a nahiyar Turai, bisa koken cewar a tsakanin shekarun 2004 zuwa 2007, kamfanin na Shell ya gurbata musu muhallinsu da hakan yayi jallin kassara sanao'insu na noma da kamun kifi, sakamakon ayyukan da kamfanin yake yi na lalubowa tare da hako danyan mai a yankin.

Matakin gudanar da wannan shari'a dai, masu fafutukar kare muhalli suka ce babban ci gaba ne a harkokin na shari'a.

A hukuncin dai da wannan kotu ta bayar a wannan Larabar (30.01.2013) kan wannan koke, kotun ta nunar da cewar lallai kamfanin shell na da rawar da ya taka a gurbatar muhalli a yankin na Neija Delta. Sai dai fa kotun ta kara da cewar halayyar 'yan fasa bututaye don satar mai a yankin na Neija Delta suma suna da laifi a matsalar ta gurbacewar muhalli a yankin, wadda dama kamfanin na Shell ya sha fadin cewar akwai zagon kasa da ake masa a yankin mai arzikin mai.

Image made available on 19 September of militants from the Movement for the Emancipation of the Niger Delta (MEND) as they patrol the volatile oil rich creeks of the Niger delta in Nigeria 18 September 2008. The Movement for the Emancipation of the Niger Delta claimed in a statement on 19 September 2008 it has attacked a pipeline operated by Shell. MEND declared 'war' on Nigeria's oil industry a week ago. EPA/GEORGE ESIRI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Kungiyar MEND da ke fafutuka a yankin Neija DeltaHoto: picture alliance / dpa

      Nasara a fafutukar kare muhallin 'yan Niger Delta

A dai hukuncin, kotun ta amince ne da bukata daya kacal cikin bukatun da manoman suka gabatar, inda ta yi watsi da bukatu hudu, tare da nunin cewar daya daga cikin manoman 4 ne kawai, wani Mr Friday Akpan zai iya samun diyya bisa hujjojin da tayi la'akari da su.

Wata mata Rachael da ke zaman makwabciyar wayannan manoma da suka kai kara akan wannan hukunci bayyana jin dadinta ne ta yi game da lamarin:

Ta ce " Abinda ya bayyana na daga wannan hukuncin kotu cewar kamfanin Shell da ke faman gurbata muhallinmu zai biya wata diyya. Na yi matikar farin cikin haka, abinda dai nake fata shine Allah yasa wannan hukunci ya tabbata a aikace, kuma hakan zai zama darasi ga kamfunan mai a yankin na cewar dole su ringa ayyukansu da kulawa."

Shi kuwa wani matashi Mr Simon da shima  ke zaman dan yankin na Neija Delta farawa yayi da cewar:

"A gaskiya kamfunan mai na yi mana barna a yankimmu ta hanyar kassara hanyoyin rayuwarmu, kuma na yi farin ciki da wannan hukunci, domin kamfanin na Shell zai san cewar shi mai laifi ne a yankin na Neija Delta."

Shi kuwa wani Aremaja Johnson shima yace ne zuciyar sa tai fari tare da godewa Allah da wannan hukunci, kuma dai da wannan hukunci, dama ce ta yadda duniya za ta kara fahimtar yadda yankin Neija Delta ke gurbata daga ayyukan wannan kamfani na Shell:

" Mun dai yi farin ciki, kuma muna fatar kyautatuwar dangantaka tsakanimmu da kamfanin da ma sauran kamfanonin mai a yankin."

Logo Royal Dutch Shell
Tambarin kamfanin Shell

        Shell yayi maraba da hukuncin biyan diyya

Bayan dai yanke hukuncin, kamfanin na Shell ya nunar DA cewar diyyar da zai bayar, lamari ne da zai zama na cimma daidaito.

Yanzu dai wannan hukunci, inji masu lura da alammura, dama ce ta budewa da daman al'ummomi a yankin na Neija Delta da suka dade suna ganin kamfanonin mai na zaluntarsu ta hanyar ayyukan da suke yi a yankin, zaluncin kuma da suke ganin sai dai suyi Allah ya isa.

Akwai dai batutuwa da dama da suka dade a kasa tsakanin kamfanin man Shell da kuma alummomi da dama a yankin na Neija Delta, musamman al'ummar Ogoni, yankin da kamfanin ya dade yana aiki ciki kafin daga bisani al'ummomin na Ogoni suyi masa tawaye, tawayen kuma da ya tilasta shi barin yankin.

Mawallafi : Muhammad Bello
Edita : Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani