1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka: Bacewar al'adar tsagen fuska

January 30, 2019

A zamanin da dai al'adar tsagen fuska ta kasance wata al'ada mai karfin gaske a cikin kabilu saboda tana daya daga cikin abubuwan da ke bambamta kabilu.

https://p.dw.com/p/3CMt5
Gesichts-Tattoo
Hoto: DW/ U. Shehu

A Jamhuriyar Nijar yankin Gaya na daya daga cikin yankunan da suka yi fice wajen girmama al'adun gado musamman ma tsagen fuska da ake iya bambamta kabilun kasar da shi. To amma sai dai sannu a hankali tsagen na bacewa tare da haifar da fargabar bacewar kabilun yankin daga 'yan gado masu kokarin kare kabilu.

A zamanin da dai al'adar tsagen fuska ta kasance wata al'ada mai karfin gaske a cikin kabilu saboda tana daya daga cikin abubuwan da ke bambamta kabilu a cewar Elhadji Manu Issifou malamin makaranta mai ritaya.

Bildergalerie afrikanische Kopftuchmode
Hoto: DW/T. Amadou

To sai dai sannu a hankali al'adar tsagen fuska na neman zama tarihi lamarin da ke da nasaba da zamani inda a cewar Illiassou Moumouni a da ana yin tsage ne don bambamta 'yan kabila a lokacin yaki yanzu kuma wannan zamanin ya rigaya ya wuce.

Daga wani bangare ma dai wayewa da kuma addini na daya daga cikin abubuwan da ke taka wa al'adar birki inji mai martaba sarkin kasar Bana Elhadji Maiki Zakari Namata.

Batun bacewar Al'adar tsage dai na daya daga cikin abubuwan da ke jawo koma baya sosai a fannin wasan tabbashi wanda 'yan kasar Nijar ke matukar tunkaho da shi.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani