Babu alamun warware rikicin Mali a nan kusa | Labarai | DW | 22.01.2013
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babu alamun warware rikicin Mali a nan kusa

Rundunar sojin Mali ta ce zai dauki kimanin wata guda kafin samun gagarumar nasara akan 'yan tawayen kasar.

Hafsan sojin Mali ya fadi a wannan Talatar (22.01.2013) cewar, dakarunsa da ke samun goyon bayan sojin Faransa za su dauki tsawon wata guda suna fafatawa gabannin kwace iko da biranen Gao da kuma Timbuktu daga hannun 'yan tawayen Mali.

Hafsan sojin ya fadi hakanne a dai dai lokacinda wasu jiragen saman Amirka suka fara jigilar karin dakarun Faransa zuwa kasar ta Mali, kana wani jami'in ma'aikatar tsaron Malin daya bukaci a sakaya sunansa ya ce sojojin Faransa sun yi ruwan bama-bamai akan sansanin mayakan 'yan tawayen da ke da ala'ka da kungiyar alQa'ida kusa da birnin na Timbuktu, mai dadadden tarihi.

Tunda farko dai kakakin ma'aikatar kula da harkokin tsaron Mali, Thierry Burkhard ya bayar da tabbacin cewar dakarun sun jefa bama-bamai a wajen birnin na Timbuktu.

Kasashen duniya na matsa kaimi wajen tallafawa Faransa da sauran dakarun kasashen yankin yammacin Afirka a gangamin da suka kaddamar na fatattakar 'yan tawayen Mali, wadanda suka yi tsawon watanni tara suna rike da iko a yankunan arewacin kasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe

 • Kwanan wata 22.01.2013
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17PuJ
 • Kwanan wata 22.01.2013
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17PuJ