1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTunusiya

Tunisiya: Abir Mussi za ta yi takara

Abdourahamane Hassane
August 3, 2024

Babbar ‘yar adawar shugaba Kais Saied na Tunisiya, Abir Moussi, da aka kulle a gidan yari tun shekara ta 2023,ta ajiye takararta a zaben shugaban kasa da za a yi a Oktoba.

https://p.dw.com/p/4j5BJ
Abir Mussi
Abir Mussi Hoto: Yassine Mahjoub/NurPhoto/picture alliance

 Abir Mussi shugabar jam'iyyart PDL ta 'yan jari huja mai ra'ayin tsofin shugabannin kasar Habib Burgiba da Zine Abdine ben Ali na shirin kalubalantar Kai Saied, wanda aka zaba a shekara ta 2019 kafin daga bisani ya yi babakere a kan mulkin. Moussi, mai shekaru 49, tsohuwar 'yar majalisar dokoki an kamata ne a ranar uku ga watan Oktoba shekarar bara. Ana tuhumarta da manyan zarge-zarge da suka hada da na nufin sauya tsarin gwamnati ta hanyar jan hankali jama'a domin bijrewa gwamnatin.