Babbar nasara a yaki da zazzabin cizon sauro | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 11.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Babbar nasara a yaki da zazzabin cizon sauro

A shekarar 2014 za a ba da lasisin samar da allurar rigakafin zazzabin cizon sauro bayan nasarar gwaje-gwajen sabon maganin yaki da cutar da ke halaka dubban mutane a Afirka.

A wannan makon jaridun sun mayar da hankali a kan batutuwa da dama na Afirka amma bari mu fara da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda a babban labarinta mai taken babbar nasara a yaki da zazzabin cizon sauro cewa ta yi.

"Bayan shafe shekaru 30 ana bincike kamfanin harhada magunguna na Glaxo Smith Kline ya samar da allurar rigakafin zazzabin cizon sauro wato Malaria ga yankuna masu zafi. Wannan wani gagarumin mataki ne da zai ceci rayukan dubban kananan yara. A kowace shekara mutane fiye da dubu 600 a nahiyar Afirka ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar ta Malaria. Daukacin wadanda cutar ke zama ajalinsu yara ne kanana da shekarunsu na haihuwa ba su wuce biyar ba. Yanzu dai kamfanin magungunan daga Birtaniya na jiran samun wani gagarumin ci gaba a yaki da zazzabin cizon sauron, domin bayan nasarar gwaje-gwajen da aka yi, a shekara mai zuwa za a ba da izinin yin allurar rigakafin cutar ta Malaria."

Kokarin magance rikicin gabacin Kwango

Sabon yunkurin samar da zaman lafiya inji jaridar Die Tageszeitung tana mai mayar da hankali a gabacin Kongo.

"Wata tawagar Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya na rangadi a kasashe da dama na Afirka da nufin farfado da tattaunawar samar da zaman lafiya da ta cije a gabacin Kwango. Tun a ranar Litinin wakilan tawagar sun kai ziyara a manyan biranen kasashen Kwango, Ruwanda da kuma Yuganda. Sannan a ranar Talata sun halarci wani zaman taron koli a babban birnin kasar Habasha wato Addis Ababa, shalkwatar kungiyar tarayyar Afirka, game da rikicin Kwangon da ya zame wa nahiyar Afirka ala-kakai. Yanzu haka dai gwamnati a Kinshasa babban birnin Janhuriyar Demokradiyyar Kwango ta yi wa 'yan tawayen kungiyar M23 dake samun goyon bayan kasar Ruwanda sabon tayi a kokarin samun maslaha a rikicin gabacin Kwango. Yanzu dai an bukaci 'yan tawayen da su kwance damarar mayakansu, sannan rundunar sojin kasar ta ce a shirye take ta shigar da mayakan kungiyar M23 su kimanin 1700 a cikinta, amma ban da kwamandojin kungiyar, domin sun sha bijire wa rundunar sojin Kwangon suna yi mata bore."

EU ta gaza a manufar 'yan gudun hijira

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland sharhi ta yi game da 'yan gudun hijira da kuma manufofin tarayyar Turai kan mafakar siyasa tana mai cewa:

"Bayan hadarin jirgin ruwan bakin haure daga Afirka da ya auku a gabar tekun tsibirin Lampedusa na kasar Italiya a farkon watan nan wanda yayi sanadiyar rayukan mutane kusan 300, kungiyar taimaka wa 'yan gudun hijira da masu neman mafakar siyasa ta Pro Asyl ba ta yarda cewa za a samu wani canji a manufar kungiyar EU da ta shafi 'yan gudun hijira ba. Domin bayan aukuwar wannan hadari ministocin cikin gidan kasashen EU kira suke da a rubanya taimakon da ake ba wa kasashen Afirka. Sai dai an jima ana irin wadannan maganganun ba tare da an ga wani sauyi mai ma'ana ba. Akasarin 'yan gudun hijirar suna tserewa daga mulkin danniya da muzgunawa da yunwa da talauci da dai sauransu. Rashin ba su damar shigowa Turai ta halattatun hanya ya sa ba su da zabi face daukar kasadar bi ta ruwa a kokarin shigowa Turai don samun wata rayuwa mai inganci. Kamata ya yi nahiyar Turai ta bude kofofinta ga 'yan gudun hijira da suka cancanta wadanda kuma ke neman taimako, amma ba a ci gaba da bin manufofi da ba sa taimakawa ba."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal