Babban taron jam'iyyar kwamunisancin Sin
November 8, 2012Talla
Shugaba Hu Jintao ya ambata hakan a Alhamis ɗin nan lokacin da ya yi wani jawabi da ya yi lokacin da ya buɗe babban taron jam'iyyarsa, inda ya ce muddin ba su tashi tsaye wajen shawo kan matsalar ba to shakka babau jam'iyyar za ta iya fuskantar matsalar da ba za su iya warware ta ba.
Mr. Hu ya ƙara da cewar dole su cigaba da kasance masu ƙwazo da riƙon amana duba da ƙudurin da su ka ɗauka na son yin gyare-gyare ga tsarin siyarsa su domin kaiwa ga nasara.
Wadannan kalamai na shugaban na kasar ta Sin na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyar ke shirin zaɓen sabbin shugabaninta da ma dai batun cin hanci da rashawa da ya yi wa jam'iyyar dabaibdayi.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammed Awal Balarabe