Ba za a yi zabe bana a Jamhuriyar Kongo ba | Labarai | DW | 10.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ba za a yi zabe bana a Jamhuriyar Kongo ba

Hukumar zabe a Jamhuriyar demokradiyyar Kongo ta ce ba za'a iya gudanar da zaben shugaban kasa dana yan majalisun dokoki a kasar kafin karshen wannan shekarar ba.

Shugaban hukumar zaben Corneille Nangaa ya shaidawa manema labarai a Kinshasa babban birnin kasar cewa zai yi matukar wuya a iya gudanar da zaben kafin watan Disamba.

A karshen wannan shekarar ce dai ya kamata a gudanar da zaben bisa yarjejeniyar da aka cimma domin kaucewa tashin hankali bayan da shugaban kasar Joseph Kabila da ya dade a karagar mulki yaki amincewa ya sauka a karshen wa'adin mulkinsa a watan Disambar bara.

Jami'yyun adawa sun soki lamirin matakin da cewa tamkar wata takalar fada ce da kuma daure wa gwamnatin gindin cigaba da zama a karagar mulki.