1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

kamanceceniyar dabi'u tsakanin Kirista da Musulmi a azumi

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
March 19, 2024

Azumin Ramadana, ibada ce da Musulmi ke gudanarwa a duk shekara, yayin da Kiristoci ke gudanar da nau'in azumin a Ista. Addinan biyu sun tanadi koyarwa da ke kamanceceniya, wanda ke zama hanyar kara samun zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/4dtc7
Addinan Musulunci na Kiristanci sun tanadi azumi ga mabiyansu
Addinan Musulunci na Kiristanci sun tanadi azumi ga mabiyansuHoto: picture-alliance/Godong/P. Deloche

A yayin gudanar da azumin Ramadana, Musulmi kan dukufa da ayyukan ibada iri-iri don neman samun kusanci ga mahalicci, inda suke sallolin farilla da nafiloli da kamewa daga ci ko sha daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana tare da bayar da sadaka ga mabukata da marasa galihu. Sannan bayan kammala kwanaki 29 ko 30 na azumin, suna gudanar da bikin sallah karama.

Karin bayani: Bikin Sallah Karama bayan kammala azumi

A bangaren Kiristoci kuwa, su kan shafe kwanaki 40 suna azumi da aka fi sani da Lent da Turanci. Dzuk da cewa yawan kwanakin kan bambanta ne zuwa darikun addinin, amma dai mabiya Katolika da wasu rukunan kan yi azumin zuwa kwanaki 40 cikin yanayi na kankan da kai da mika wuya ga ubangiji domin neman gafararsa kan zunuban da mutum ya aikata. Sannan bayan kammalawa, Kiristoci na bikin Ista.

Wani Musulmi da iyalinsa a lokacin shan ruwa na watan azumin Ramadana
Wani Musulmi da iyalinsa a lokacin shan ruwa na watan azumin RamadanaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Maikatanga

Lokacin azumin Ramadana, Musulmi kan daina cin komai da zarar alfijir ya keto, kuma su kan kasance masu kankan da kai da jin kan marayu da gajiyayyu don gode wa rahamar ubagiji a ko yaushe. Yayin da su kuma Kiristoci ke kaurace wa wasu nau'ika na abinci da barasa da nama da dai sauransu, a matsayin tunawa da sadaukarwar da Yesu Almasihu ya yi a cikin saharar Judean da ke yammacin Isra'ila.

Karin bayani: Azumi cikin tsadar rayuwa a Afirka

Azumin Ramadan na koyar da Musulmin duniya hadin kai da taimakon juna, inda ake ganin wasu na shirya taron shan ruwa da kyaututtuka da makamantansu. Sheikh Ali 'Dan Abba malamin addinin Musulunci a Kano da ke tarayyar Najeriya ya ce Musulunci ya yi horo da zaman lafiya. Su ma Kiristoci kan yi kyaututtuka da gudanar da ayyukan hadin kan juna a duniya, kamar yadda Reverend Yuguda Zibagainduruwa malamin addinin Kirista a jihar Bornon tarayyar Najeriya ya bayyana.

Kiristoci na adu'o'i a majami'u bayan azumin Lent
Kiristoci na adu'o'i a majami'u bayan azumin LentHoto: Reuters/S. Dawson

Duka addinan biyu sun yi tanadin dukufa wajen neman kusanci da ubangiji a wannan lokaci na azumi. A don haka akwai bukatar Musulmi da Kirista a fadin duniya su yi amfani da wadannan nau'ikan dabi'u masu kamanceceniya da juna da addinansu suka koyar, wajen girmama juna da kara dankon zumunci a tsakanin juna cikin kwanciyar hankali da lumana.

Karin bidiyo: 

Gaskiyar Magana: Abincin da ya kamata a ci a Ramadan