1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Awa ashirin da hudu, kwana daya

Abba BashirAugust 29, 2005

Raba Rana zuwa awa ashirin da hudu a matsayin kwana daya

https://p.dw.com/p/BwXR
Agogon Birnin Landan
Agogon Birnin LandanHoto: AP

Masu sauraron mu asalamu alaikum barkan mu da sake saduwa cikin wani sabon shirin na amsoshin takardun ku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

TAMBAYA: Fatawar mu ta wannan makon ta fito daga hannun mai sauraron mu Mallam Zulkifli Muhammad, B.P.1319 ,Bangui, Afirka ta tsakiya.Yace shin me yasa aka raba Rana zuwa awa ashirin da hudu, ba awa Takwas ko Goma-sha-uku ba?

AMSA: Raba Rana ya zuwa awa ashirin da hudu amatsayin kwana daya, za’a iya bin diddigin asalinsa tun lokacin Tarihin Misirawa da kuma mutanen Kasar Babila, tun kusan shekaru dubu hudu da suka wuce,sakamakon kokarin da suka yi na dora Duniya akan wani kiyasi na lokaci da aka fi sani da suna “Analog Clocks’’ a Turance.

A wancan lokaci Misirawa masana ilimin Taurari sun yi kokarin raba awannin dare na kwana guda zuwa aji-ajin Taurari guda goma sha biyu. Sannan kuma sai suka raba tsawon wuni guda shima zuwa awa goma sha biyu domin yayi dai dai da dare. Kasancewar su Misirawan, suna kusa da layin da ya raba Duniya gida biyu wanda aka fi sani da suna “Equator’’a Turance, sai ya kasance dare da rana kusan tsawon su daya a gabadayan shekara, wato Rani da Damina.

A sauran gabakidayan Kasashen Duniya kuwa, tsawon awanni na Dare da Rana ya na canjawa tsakanin lokacin sanyi da lokacin zafi. Misali kamar a Kasashen turai, inda awa daya ta rana ta ke kusan ninka awa daya ta dare a lokacin zafi.

Ba’a dai samu an daidaita tsakanin awanni ba har sai a karni na goma-sha-uku {13 } lokacin da Allah ya kawo wani Balarabe masanin ilimin kimiyya da a ke kira da suna Abul-Hassan wanda ya kirkiro fasahar daidaita tsawon awanni daidai wa daida, wato akan minti sittin ga kowacce awa.

A sane ya ke dai a tarihi cewa, {12} lamba ce ta musamman ga mafia yawan al’ummomi, misali Misirawa suna yin lissafinsu ne a karkashin tushen lamba {12} . kuma raba kwana daya zuwa ga awanni goma sha biy-biyu wata sassaukar hanya ce ta hikima, wajen takaita watannin shekara guda goma sha biyu zuwa wuni daya.