1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ostireliya ta nemi afuwan yaran da aka ci zarafinsu

Ramatu Garba Baba
October 22, 2018

Firaiministan kasar Ostireliya Scott Morrison ya nemi afuwa daga dubban yara da aka aikata lalata da su a sassan kasar, cikin yanayi na kaduwa ya baiyan takaici kan wannan bala'in da ya ce ya rutsa da yara kanana.

https://p.dw.com/p/36vOr
Australien Parlament Scott Morrison Entschuldigung Missbrauchsopfer
Hoto: Getty Images/AFP/S. Davey

A jawabinsa na wannan Litinin a zauren majalisar kasar, Firaminisa Scott Morrison na Ostireliya ya ce a matsayin mu na kasa mun amince da gazawarmu a jan kafa da aka samu na sauraron koken wadanda suka nemi fadin gaskiya kan halin da 'ya'yanmu suka fada a hannun limaman coci ba tare da mun iya ceto su daga wannan bala'i ba.

Wannan na zuwa ne, shekara guda bayan da bincike wata hukuma mai rajin hana cin zarafin yara, ya gano cewa,  kashi bakwai cikin dari na malaman katolika sun yi lalata da yara a tsakanin shekarun 1950 da 2010 a kasar. Bayan jawabin ministan, wasu daga cikin wadanda aka ci zarafinsu, sun nuna gamsuwa wasu kuwa sun ce ihu ne kawai bayan hari.