Austalia zata aike da dakarun sojin kiyaye zaman lafiya izuwa E Timor | Labarai | DW | 25.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Austalia zata aike da dakarun sojin kiyaye zaman lafiya izuwa E Timor

A wani lokaci ne a yau din nan kasar Austaralia zata aike da bataliyar soji 150 na kiyaye zaman lafiya dake a matsayin zangon farko izuwa kasar Timor ta gabas.

Dakarun sojin kiyaye zaman lafiyar dai zasu isa babban birnin kasar ne wato Dili don taimakawa wajen murkushe aiyukan bijirarrun sojin kasar.

A gaba daya dai a cewar faraministan kasar ta Austaralia, wato John Haword, kasar zata tura da dakarun soji izuwa kasar ta Timor ta gabas ne a kalla dubu 1 da dari 3 , tare da kana nan jiragen yaki na ruwa dana sama.

Rahotanni daga kasar sun nunar da cewa an kara fuskantar Dauki ba dadi a tsakanin dakarun sojin Timor ta gabas din da kuma bijirarrun sojojin a can gabashin kasar.

Wannan arangama da a yau ta shiga kwana na uku, ya zuwa yanzu an sanar da asarar rayuka uku san nan mutane takwas sun jikkata.

Kasar dai ta Timor ta gabas ta fada rikici ne a tun bayan da aka yiwa wasu sojin kasar 600 murabus daga aiyyukan su, bayan kokarin da suka yi na cewa ana nuna musu wariyar launin fata.