Aung San Suu Kyi na hanyar kafa tarihi | Labarai | DW | 09.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Aung San Suu Kyi na hanyar kafa tarihi

Jam'iyyar Aung San Suu Kyi ta Myammar ta yi ikirarin lashe kashi 70 daga cikin 100 na kujerun majalisa, duk da cewa ba a bayyana sakamako a hukumance ba.

Jam'iyyar NLD ta madigar 'yan adawan Myammar ko Bama Aung San Suu Kyi ta bayyana cewa ta kama hanyar kafa tarihi a kasar sakamakon gagarumin rinjaye da ta samu a zaben da ya gudana a karshen mako. Kakakin wannan jam'iyya Win Htein ya bayyana wa kanfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa sun lashe fiye da kashi 70% na kujerun majalisa, ko da shi ke dai har yanzu hukumar zabe ba ta bayyana sakamakon ba.

Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 25 da suka gabata da aka shirya zabe bisa tafarkin demokaradiya a Myammar. Tuni ma dai gwamnatin wannan kasa da sojoji ke babakere a cikinta ta bayyana cewa za ta mutunta sakamakon wannan zaben ko da ta sha kaye.

Ita Aung San Suu Kyi da ta taba samun lambar yabo ta Nobel ta nuna sha'awar jagorantar sabuwar gwamnati idan jam'iyyarta ta samun gagarumin rinjaye.