1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU za ta daina ba da rigakafin AstraZeneca

April 8, 2021

Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta bayar da sanarwar jingine batun samawa kasashe mambobinta alluran rigakafin COVID-19 kirar kamfanin AstraZeneca.

https://p.dw.com/p/3rkIt
Bangladesch AstraZeneca Impfung
Hoto: Mortuza Rashed/DW

Hukumar da ke kula da cututtuka masu saurin yaduwa ta kungiyar, ta ce saukin ta'ammali da alluran kamfanin AstraZeneca ne ya bai wa kungiyar wannan zabin wanda ya yi daidai da yanayi da kuma bukatun kasashe masu tasowa.

Haka zalika sanarwar ta zo kwanaki 2 bayan da takwararta ta Tarayyar Turai ta ce ta gano cewa allurar ta kamfanin AstraZeneca na da ruwa da tsaki wajen haddasa dunkulewar jini wanda ya zama tilas a kare al'umma.

Kungiyar ta AU har ila yau, ta dauki wannan matakin ne daidai lokacin da hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta bakin daraktanta na yankin Afirka Matshidiso Moeti ke koka wa dangane da yadda aka bar kasashen nahiyar baya wajen yin rigakafin. 

Kawo yanzu a iya cewa AU din ta yi fargar jaji, bayan da mafi yawancin rigakafin da ake amfani da ita a yankin ta kamfanin ce wadda aka samar karkashin shirin COVAX na WHO.