Shugaban WikiLeaks Julian Assange ya yi nasarar samun izinin daukaka kara, kan hukuncin mika shi ga kotun Amirka, don cigaba da tuhumarsa kan zargin wallafa sirrin gwamnati.
A watan Disamba na shekarar 2021, wata babbar kotu a birnin Landan ta yi watsi da hukuncin da wata karamar kotu ta yanke na kin tura Assange kasar Amirka bisa hujjar cewa zai iya kashe kansa.
Gwamnatin Washington na son a gurfanar da Julian Assange dan Australia mai shekaru 50 a gaban kuliya a kasarta, bisa zargin buga bayanan sirri na Wikileaks 500,000 da suka shafi yake-yaken da kasar Amirka ta shiga a kasashen Iraki da Afghanistan.