1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunisiya: Gangamin yakin neman zabe ya kankama

Abdullahi Tanko Bala AMA
September 13, 2019

Gwagwarmayar zaben ranar Lahadi da za a gudanar a Tunisiya ya banbanta da wanda aka saba gani, salon yakin neman zaben da ma batutuwan da suka dauki hankalin jama'a sun sha banban da na baya.

https://p.dw.com/p/3PXwo
Tunesien | Präsidentschaftswahlkampf | Wahlplakate in Tunis
Allunan tallata wasu 'yan takara a zaben shugabancin kasa a TunisiyaHoto: Getty Images/AFP/F. Belaid

Wata daya da rabi bayan rasuwar tsohon shugaban Tunisiya Beji Caid Essebsi jama'ar kasar za su koma rumfunan zabe domin zabar sabon shugaban kasa. Kundin tsarin mulkin kasar ya bada damar nada shugaban riko na tsawon watanni uku ne kacal. Da farko dai an shirya gudanar da zaben ne a farkon watan Oktoba kafin daga bisani a daga zuwa 15 ga watan Satumba.Yan takara 26 ne ke neman wannan mukami, kuma daya daga cikinsu shine Nabil Karoui wanda a yanzu haka yake tsare a gidan yari. Makonni biyu da suka wuce ne aka kama Nabil karoui wanda ya mallaki gidan talabijin mai zaman kansa mafi girma a Tunisiya bisa tuhumar sa da laifin kaucewa biyan haraji da kuma safarar kudaden haramun. To amma sai dai kamen da aka yiwa Karoui ya haifar da cece-kuce a Tunisiya.

Matasa da yaki da talauci na kan gaba a yakin neman zabe

Tunesien | Präsidentschaftswahlkampf | Anhänger Tahya Tunis
Magoya bayan wata jam'iyyar da ke takaraHoto: Getty Images/AFP/Hasna

Daga cikin masu yakin neman zaben har da jam’iyyar islama da ta jima tare da gwamnati tun shekarar 2014 sannan a daya bangaren an sami sabon dan takara wanda ba za a iya danganta da shi da cewa yana daga cikin masu ra’ayin addini ko kuma babu ruwansa da addini ba. A takaice dai yanayi ne yazo wanda dole yan siyasa su yi magana akan abin da ya shafi rayuwar jama’a na yau da kullum, kamar batun tattalin da rashin aiki. Saboda haka a wannan karon talauci da makomar rayuwar matasa sune jigon batutuwan yakin neman zabe wanda ya banbanta da na baya, daga ciki har da na dan takarar Jam’iyyar En-Nahda Abdelfattah Mourou wanda ke cikin gwamnati tun shekarar 2014 kuma ya kasance mai ra’ayin mazan jiya. A bana yanayin yakin neman zabensa ya bamnbanta da yadda aka saba gani a baya.

Jamus na bin kadin yadda za a gudanar da zaben

Wahlen in Tunesien
Turawan zabe na duba kuri'un zaben 2014Hoto: Reuters

Kasar Jamus ta sa ido kan zaben da kuma sakamakon da zai biyo baya. Tunisiya ta fi kowace kasa samun taimakon raya kasa daga gwamnatin Jamus. Inda kuma Jamus ta ce tana son ganin Tunisiya ta kama hanya sannu a hankali don tabbatar da dorewar dimokradiyya a kasar ta arewacin Afirka.