Ashraf Ghani shi ne zababben shugaban kasar Afganistan
September 21, 2014Talla
'Yan takaran shugaban kasa biyu a kasar ta Afganistan da suka fafata da juna a zagayen karshe, sun sa hannu domin kafa gwamnatin raba iko, watanni da dama bayan kammala zaben. Ashraf Ghani wanda aka bayyana a matsayin shugaban kasa, ya rungumi abokin hammayarsa Abdallah Abdullah, wanda ake saran zai rike mukami mai kaman na Firaminista. Ya yin sa hannun a yarjejeniyar a samu halartan shugaba mai barin gado Hamid Karzai, inda kuma aka yada sa hannu kai tsaye a kafafen yada labaran kasar. Sabuwar gwamnati da za'a kafa a Afganistan za ta fiskanci kalubale, musamman yanzu da mayakan Taliban suka zafafa hare-hare da kuma talaucin da ya addabi kasar.