Asarar dukiya da rayuka yayin hari a jihar Adamawa | Labarai | DW | 09.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Asarar dukiya da rayuka yayin hari a jihar Adamawa

Harin 'yan bindiga ya hallaka mutane da dama a Adamawan tarayyar Najeriya.

Wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari kan kauyen Fotta da ke da yamma da garin Gombi da ke arewacin jihar Adamawan tarayyar Najeriya inda suka hallaka mutane 5 tare da kone ofishin 'yan sanda da kotu da wasu majami'u 2 da ke a yankin.
Harin wanda aka kai shi cikin daren wannan Asabar, ya ritsa da taron wani aure inda aka yi kisa tare jikkata wasu da dama.
Cikin zantawarsa ta wayar tarho dawakilinmu na jihar ta Adamawa Muntaqa Ahiwa, wani mazaunin yankin ya bayyana halin fargabar da jama'a ke ciki.
Tuni dai jami'an tsaron jihar ta Adamawa suka tabbatar da faruwar wannan harin wanda ke zaman karo na hudu da aka kai irinsa a yankin.

Mawallafi : Muntaqa Ahiwa

Edita : Saleh Umar Saleh