Archibishop Desmond Tutu ya koma gida | Labarai | DW | 21.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Archibishop Desmond Tutu ya koma gida

Dan tahaliki da ya samu lambar yabo ta zaman lafiya a duniya, na da shekaru 83 ne sannan an maida shi asinbiti ne a makon da ya gabata bayan harbuwa da wasu kwayoyin cuta.

Deutschland Desmond Tutu in Lübeck

Desmond Tutu malamin majami'a dan fafutika

Wata kungiyar agaji da jinkai da kare hakkin bil'Adama a kasar Afirka ta Kudu ta bayyana cewa babban malamin majami'ar nan archbishop Desmond Tutu ya koma gida bayan mako guda a asibiti bisa umarnin likita da ya nemi ya zauna ya huta. A jawabin da cibiyar Desmond and Leah Tutu ta fitar, ya nunar da cewa babban malamin majami'ar ya koma gida ne a ranar Talatan nan.

Iyalan archibishop Tutu sun bayyana godiyarsu ga likitoci da ma sauran jama'a saboda nuna musu kauna da suke yi.Dan tahaliki da ya samu lambar yabo ta zaman lafiya a duniya, na da shekaru 83 ne sannan an maida shi asinbiti ne a makon da ya gabata bayan harbuwa da wasu kwayoyin cuta amma ya samu sauki bayan ya sha magunguna nau'in antibiotics.

A cewar 'yarsa Mpho Tutu rashin lafiyar da mahaifinta ya samu aka kai shi asibiti a wannan lokaci ba ta da alaka da ciwon da yake fama da shi na daji da kan kama maraina, shekaru 18 kenan da ya samu cutar.