1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Antonio Guterres zai ziyarci Butcha

Abdourahamane Hassane
April 28, 2022

Baban sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres zai isa a Butcha da ke da tazarar kilomita 30 daga arewa maso yammacin babban birnin Ukraine, wato Kiev.

https://p.dw.com/p/4AXQW
Russland Moskau UN Generealsekretär Antonio Guterres
Hoto: Maxim Shipenkov/REUTERS

Sakataran Majalisar Dinkin Duniyar ya isa a Ukraine daga birnin Moscow inda ya roki Vladimir Putin da ya tsagaita bude wuta. Guteres ya ce ya damu matuka da rahotannin da ake ta yi na yiwuwar aikata laifukan yaki, yana mai cewa suna bukatar bincike mai zaman kansa. Sannan zai tattauna da shugaban Ukraine ganin  ta yadda za a ceto farar hula da suka makele a birnin Mariuopol.