1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ansaruddine na shirin mika wuya a Mali

November 6, 2012

Kungiyar Ansaruddine ta arewacin Mali ta ce a shirye ta ke ta bayar da kai domin bori ya hau, a daidai lokacin da ake shirin afka ma ta domin kubutar da yankin da ke hannunta.

https://p.dw.com/p/16dqd
Hoto: Reuters

Kungiyar Ansaruddine da ke da tsananin kishin addini ta ce a shirye ta ke ta tattauna da hukumomin Mali domin samar da maslaha ga rikicin da kasar ta shafe watannin ta na fuskanta. Ita dai wannan kungiya da yankin Arewacin Mali ke karkashin ikonta, ta bayyana matsiyan na ta ne bayan da ta shafe kwanaki uku ta na tattaunawa da hukumomin kasar Aljeriya. Sai dai kuma Ansaruddine ta nesanta kanta daga duk wasu ayyukan ta'addanci a yankin Sahel da kuma garkuwa da mutane da ake alakanta ta da su.

Masu kaifin kishin addinin na Mali suna tattaunawa da hukumomin Aljeriya da kuma na Burkinsa Faso, a daidai lokacin da kasashen yanmmacin Afirka ke shirin afka musu domin kubutar da yakin arewacin Mali . Babban mai shiga tsakani a rikicin wato shugaba Blaise Compaore na Kasar Burkina faso ya na neman Ansaruddine ta raba gari da kungiyoyin Aqmi da kuma Mujao da ke gudanar da aiyukan ta'adanci. Yayin da fadar mulki ta Alger ta ke neman kungiyar ta hau kan teburin tattaunawa domin warware rikicin arewacin Mali cikin ruwan sanyi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu