Ansaru ta hallaka ′yan kasashen ketare da ta yi garkuwa da su a Najeriya | Labarai | DW | 10.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ansaru ta hallaka 'yan kasashen ketare da ta yi garkuwa da su a Najeriya

Gwamnatocin kasashen Italiya da Birtaniya sun tabbatar da kashe 'yan kasashensu a yankin arewacin Tarayyar Najeriya.

Gwamnatocin kasashen Italiya da Birtaniya sun tabbatar da kashe 'yan kasashen, da ke cikin wadanda wata kungiya ta yi garkuwa da su, a yankin arewacin Tarayyar Najeriya, a watan da ya gabata.

Mutanen bakwai da aka hallaka bayan garkuwa da su, sun hada da 'yan kasashen: Birtaniya, Italiya, Girka da Lebanon. Kungiyar ta Ansaru mai da'awa da sunan addinin Islama, ita ce ta bayyana kisan bayan garkuwa da mutanen.

Ministan harkokin wajen Birtaniya William Hague cikin wata sanarwa ya ce, akwai yiwuwar cewa an hallaka mutanen bayan garkuwan. Firaministan Italiya Mario Monti ya ce gwamnatin kasar za yi duk abun da ya dace, domin gurfanar da masu garkuwan a gaban kotu.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi