1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ansar Dine ta yi watsi da ayyukan tarzoma

November 9, 2012

Matakin yin fatali da tashe tashen hankula na da muhimmanci a ƙoƙarin gano bakin zaren wareware rikicin Mali.

https://p.dw.com/p/16g3h
Hoto: AFP/Getty Images

A wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan ƙasar Mali. A labarinta mai taken alamun warware rikicin Mali a siyasance jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi:

"A tattaunawar da ta yi da masu shiga tsakani a ƙasar Burkina Faso, ƙungiyar Ansar Dine mafi muhimmaci a jerin ƙungiyoyi dake rikici a arewacin Mali ta amince ta yi watsi da ayyukan tarzoma. A lokaci ɗaya kuma shugabannin ƙasashen yammacin Afirka sun amince da shirin tura sojojin da za su yaƙi ƙungiyoyin Islama a arewacin ƙasar ta Mali. Wannan mataki da ƙungiyar ta Ansar Dine ta ɗauka na yin watsi da dukkan ayyuka na tsattsauran ra'ayi da ta'addanci kana ta yarda ta shiga yaƙi da masu aikata miyagun laifukan na tsallaken iyaka don magance rikicin ƙasar Mali da ta rarrabu, yana da muhimmanci."

A sharhin da ta yi game da halin da ake ciki a Mali, jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara ne da cewa wajibi ne nahiyar Turai ƙara zage damtse, sannan sai ta ci gaba kamar haka:

"Ba wanda ya san yawan sojojin Mali, amma abin da ke a fili shi ne suna cikin hali mawuyaci ga karayar zuciya ga kuma rashin isassun kayan aiki, saboda haka su kaɗai ba za su iya yaƙar masu kaifin kishin Islama dake arewacin ƙasar ba. Bai kamata aikin sojojin ƙasashen Afirka da za a tura Mali ya ruguje ba, domin akwai babban hatsari cewa arewacin Mali ka iya zama wata tungar masu matsanancin ra'ayi. Sai dai hakan ba ya nufin dole nahiyar Turai ta tura dakaru, amma wajibi ne ta shiga a dama da ita a ƙoƙarin gano bakin zaren warware rikici. Saboda da haka daidai ne da ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ba da fifiko ga muhimmancin magance matsalar Mali a siyasance. Sai dai kuma dole ne a tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro."

Westerwelle ya yaba da yaƙi da ayyukan tarzoma da Najeriya ke yi, har wayau inji jaridar Süddeutsche Zeitung ta na mai nuni da ziyarar da ministan harkokin wajen na Jamus ya kai birnin Abuja a cikin rangadin ƙasashen Afirka da ya yi a makon da ya gabata. Ta ce:

"Ziyarar ta zo ne a lokacin da ƙungiyar Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da keta haƙƙin bil Adama a matakan da take ɗauka a yaƙin ƙungiyar nan da ake kira Boko Haram. Ministan harkokin wajen na Jamus ya san ba zai iya kawar da kai daga wannan zargi ba kasancewa shi da kanshi ne ya yaba da yaƙin da Najeriya ke yi da 'yan tarzoma a cikin ƙasar, har ma ya yi mata alƙawarin ba ta taimakon bisa manufa. Shi yasa yayi taka tsantsan a tsokacin da yayi kan wannan zargi yana mai cewa rahoton na Amnesty International mai tayar da hankali ne amma Jamus ba ta da wata masaniya kuma har izuwa lokacin da aka wallafa rahoton ba a yi wa Jamus wani ƙarin bayani ba."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Mouhamadou Awal Balarabe