1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annobar Sidar Ayaba a Kwango

Zulaiha Abubakar
March 27, 2018

Manoman Ayaba da ke yankin gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango na neman mafita daga mahukuntan kasar sakamakon bullar wata annoba mai lakabin Sidar Ayaba wacce take kassara noman Ayaba a yankin.

https://p.dw.com/p/2v4z2
Kammspinne Bananenspinne
Hoto: picture alliance/dpa/R. Koenig

Bweremana gari ne da manoma ayaba suka yi sansani a jamhuriyar demokradiyyar kwango wanda kuma a halin yanzu suka tsinci kansu a wani yanayi na tsaka mai wuya sakamakon wata annoba da take lalata ayaba tun daga gona:

kwayar cutaR mai suna Wilt Bacteria wacce manoma ke yi mata lakabi da cutar Sidar Ayaba likitocin gona sun ce ta samo asali ne daga wata tsuntsuwa wacce ta taso daga wani yanki na Amirka zuwa kasar Habasha kafin daga bisani ta sauka a garin na Bwere da ke kasar Kwango a shekara ta 2004, a lokacin da bishiyar Ayaba ke mamaye da kashi 70 na kasar dake fadin yankin arewacin Kivu lamarin da a halin yanzu ya canza kamar yadda Jovite Balera yayai karin haske.

"A lokacin da wannan annoba ta lakume gonakin Ayaba, masana a kan wannan kwayar cuta sun kawo mana ziyara, sun kuma umarce mu da mu sare duk wata bishiyar Ayaba da muka ga alamar ta kamu, sannan kada muyi wa wata lafiyayyiyar bishiyar amfani da gatarin da muka sare wacce ta kamu har sai mun tsoma cikin wani magani da zai kashe kwayar cutar jikinta.

Masu bincike daga ma'aikatar gona a kasar ta Kwango hadin gwiwa da cibiyar abinci da amfanin gona ta Majalisar Dinkin Duniya sun kimanta asarar noman Ayabar wannan shekara da kashi 27 cikin dari a bangaren manoma da kuma asarar dalar Amirka 2000 a kowanne gida kowacce shekara duk a dalilin wannan kwayar cuta ta Sidar Ayaba. Lamarin da ya tilastawa kasar shigowa da Ayaba daga kasar Ruwanda ita ma Jeanini na daya daga cikin manoman da wannan annoba ta lakumewa Ayaba tun daga gona.

Ta ce "A baya gona ta makare take da Ayaba kuma da ita na dogara ni da iyalina, to amma duk mun sare su kuma matsalar ma ita ce ba zamu iya dasa wasu ba, mun gwada maye gurbinta da Kabeji da kuma Dankalin turawa amma abin yaci tura.

A halin yanzu a iya cewa manoman na ayaba a Kwango na kyakkyawan fatan wannan magani zai kakkabe sidar Ayaba a fadin kasar don tattalin arzikin su ya cigaba da habaka.