1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar amai da gudawa a sharhukan jaridun Jamus

Usman Shehu Usman AMA
August 27, 2021

Cutar amai da gudawa da ta barke a yankin arewacin Najeriya da yakin ta'addanci a yankin Sahel sun mamaye jaridun Jamus a sharhukansu kan nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/3za32
Choleraausbruch in Simbabwe
Wasu likitoci na sa ido kan masu cutar amai da gudawa Hoto: picture-alliance/dpa/T. Mukwazhi

Za mu fara ne da jaridar die Tageszeitung, wace ta yi labarinta kan yaduwar cutar amai da gudawa a Najeriya wacce ta bude labarinta da aza ayar tambaya. Batun corona kuke yi to a nan muna fama da cutar amai da gudawa sai kuma Ebola. Sai jarida ta kara da cewa a Najeriya kama daga farkon bana mutane 1.172 suka mutu sakamakon cutar amai da gudawa "Cholera" wannan bisa alkaluman da cibiyar kula cututtuka ta kasar ta fitar, inda cibiyar tace a hukumance mutane 37.819 suka kamu da cutar kawo yanzu. A jihar Bauchi kawai mutane 773 aka tabbatar da sun kumu da cutar amai da gudawa wanda babu jihar da ta taba samun yawan kamuwa da cutar kamar haka a fadin Najeriya. Yayinda cutar tafi addabar jihohin arewacin kasar die Tageszeitung, tace a yanzu jihohi 23 cikin 36 na Najeriya duk an samu bullar cutar amai da gudawa. 

Fargabar yankin Sahel ya kasance tamkar Afghanistan.

Frankreich | G5 Gipfel | Präsident Emmanuel Macron
Shugaban Faransa da na Nijar a taron G5 Sahel na watan YuliHoto: Stephane de Sakutin/AP Photo/picture alliance

Shin ko yankin Sahel zai kasance wata sabuwar Afganistan? Wannan shi ne babban labarin jaridar der Freitag, inda jaridar ta ce yanzu akwai dakuran Tarayyar Turai da ke aikin samar da zaman lafiya a Sahel na kuma aiki irin wanda suka yi a Afganistan wato yaki da ta’addanci. To amma lamarin a yankin Sahel na cike da sarkakiya. Wani manomi a kasar Mali ya fada wa jaridar cewa, yanzu talakawa sun shiga tsaka mai wuya, domin idan sojojin kasashen Yamma sun kama wani da sunan ta’addanci sai ‘yan tadda su dira kan fararen hula, da zargin cewa su suka tsegumta wa dakarun har suka kama wanda ake tuhuma. A kauyen arewacin Mali da wannan yake, a makwanni da suka gaba kimanin mutane 51 suka mutu bayan fashewar bama-bamai, don haka mazauna yankin a yanzu ke cewa su fa basu yi imanin cewa sojojin kasashen Yamma na kare su daga ‘yan ta’adda ba, haka kuma basu yi imanin cewa sojojin na yaki da ‘yan tadda masu alaka da al-Qa’ida ba.

Makomar sojojin Jamus da na kasashen Turai a Sahel

Frankreich Mali - Militär Konflikte
Wani sojan Turai da na Mali a arewacin MaliHoto: Frederic Petry/Hans Lucas/picture alliance

Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta yi labari kan yaki da ta’addanci a yankin Sahel. Jaridar ta ruwaito wakilin shugabar gwamnatin Jamus kan harkokin Afirka Günter Nooke na mai cewa, abinda ya kai su Afirka batu ne na taimakawa tattalin arzinkin Afirka. Jaridar ta ce bayan da batun wanzar da zaman lafiya a kasar Afganistan ya zama aikin wofi, yanzu hankula sun karkata zuwa Afirka inda canma kasashen yamma ke da dakaru masu aikin na yaki da ta’addanci. Jarida ta aza ayar tambayar cewa shin mene ne makomar sojojin kasar Jamus da na kasashen Turai aiyukan da suke yi yanzu a nahiyar Afirka? An san da jimawa ana tura dakaru kuma kudi na tafiya musamman a yankin Sahel da sunan yaki da ta’addanci, shin an samu zaman lafiyan? Sai kuma jaridar ta ruwaito wakilin shugabar gwamnatin Jamus kan harkokin Afirka Günter Nooke na mai cewa bayan haushin da aka ji na yadda aikin wofi da suka yi a Afganistan, dole yanzu darasin da suka koya shi ne rika tunanin zahirin aikin sojojin da ake tura wa a kasashen waje.

Rashin aiki ya karu ya kuma kusa mamaye kasar Afirka ta Kudu 

Südafrika Rustenburg Mine Streik Bergarbeiter
Matasa na bore a Afirka ta KuduHoto: Getty Images

A labarinta jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ruwaito cewa kasar Afirka ta Kudu ita ce ta fi yawan marasa aiukin yi a duniya. Jaridar ta ce musamman yanzu da corona ta zo ta kara munanan lamarin fiye da tunani. Jaridar ta yi misali da birnin Cape Town, inda tace shugana da wuraren sayar da abinci duk wayam ka ke gani wasu sun zama kango, kuma haka lamarin yake a sauran biranen kasar, har zuwa tsakiyar wannan shekarar alkulama sun nuna rashin aikin yi ya karu da kashi 34 wanda su ne mafiya yawa a fadin duniya cikin karamin lokaci, domin kasar Girka da ke zama ta biyu kashi 15 ckin dari ne aka samu na karuwar rashin aikin yi.  

Zamu kare sharhin jaridun da batun Husnah Kukundakwe, ‘yar kasar Yuganda wace ta kasance mafi karancin shekaru a gasar nakasssu na Olypic da ke gudanana a Japan. Jaridar die tageszeitung ta ruwaito Husnah yar shekaru 14 da haihuwa na mai cewa ita fa ba wai sai ta ci kyauta ba, amma kasacewar ta samu shiga gasar kawai ya isheta kyauatar. Yar shekaru 14 ta na cikin masu guje-guje da tsalle tsalle na bana.