Annan ya juya baya kan rikicin Siriya
August 2, 2012Kofi Annan ya ajiye aiki a matsayin mai shiga tsakani na rikicin Siriya, saboda rashin goyon baya daga sassan da ke da hannu a cikin rikicin.Tsohon sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Annan, ya zargi Majalisar da rashin bashi giyon bayan da ya bukata.
"A lokaci da mu ke cikin buƙata, lokacin da al'umar Siriya ke neman taimako, amma babu sai sa-in-sa kawai ake samu a Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya."
Mr. Annan wanda ya kuma ce ko ba daɗe ko ba jima gwamnati Shugaba Bashar al-Assad za ta faɗi. Wannan ya ajiye aiki ya zo lokacin faɗa ya ƙara dagule cikin ƙasar ta Siriya.
A cikin wani martani ƙasar Rasha ta nuna kaɗuwa da yadda Kofi Annan ya ajiye aiki ba zato ba tsammani, kan rikicin na watanni 17, kamar yadda jakadan ƙasar da ke MƊD Vitali Churkin ya bayyana. Amma Amurka ta ce haka ya nuna gazawar Shugaban Bashar al-Assad, da kuma yadda China da Rasha su ka kasa goyon bayan shirin Kwamitin Sulhu na Majalisar ta Ɗinkin Duniya.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal