ANC ta yi wa shugaba Zuma kiranye | Labarai | DW | 13.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ANC ta yi wa shugaba Zuma kiranye

Jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta Kudu ta sanar da yi wa shugaba Jacob Zuma mai fama da badakalar cin hanci da sama da fadi da dukiyar kasa kiranye daga mukaminsa.

Sai dai babban sakataren ANC ta kasa Ace Magashule ya ce, basu tsayar masa da wa'adin ranar da zai yi murabus ba, dangane da wannan mataki da kwamitin gudanarwar  jam'iyyarsu ya zartar, bayan tsawon lokaci.

Tun da farko dai Magashule ya sanar da cewar, shugaba Zuma ya amince da yin murabus, amma ya nemi a barshi ya cigaba da zama a kan mulki na tsawon wasu watani, batun da jam'iyyar ANC ta yi watsi da shi.

Al'ummar Afirka ta Kudun dai na cigaba da yin martani, sai dai mafi yawa na muradin Zuma ya sauka kamar  wannan 'yar kasar Kebolokile Morobisi.

" A gaskiya mun gaji da wannan badakala na cin hanci da rashawa a kasarmu, kuma ina ganin saukar shugaba Zuma daga mulki zai taimaka mana matuka wajen ciyar da kasrmu gaba. Lokaci ya yi da zai koma gefe guda, domin ya jagoranci kasarmu na tsawon shekaru 9. Don haka Baba zuma lokaci ya yi ka sauka, ka huta kamar Mugabe a Zimbabwe".