1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guinea Conakry : Al'umma na zaben sabon shugaba

Abdoulaye Mamane Amadou
October 18, 2020

Al'ummar kasar Guinea Conakry fiye da mutun miliyan biyar na gudanar da zaben shugaban kasa da ke zaman irinsa na farko mai tattare da hadarin ringingimu.

https://p.dw.com/p/3k675
Guinea Präsidentschaftswahl 2020 Conakry
Hoto: Cellou Binani/AFP

Yan takara 12 ne ke shirin fafatawa a yayin zaben na yau ciki har da Alpha Conde mai shekaru 82 da ke neman zarcewa akan madafan ikon kasar biyo bayan ya yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska.

Masu nazari kan al'amurra na ganin fafatawar zata fi zafi ne tsakanin shugaba Conde da babban abokin hamyyarsa tun a shekarar 2010, wato Cellou Dalein Diallo madugun 'yan adawar kasar mais shekaru 68 a duniya, da kuma ya shafe tsawon lokaci yana kai ruwa rana da shugaban mai hankorin tazarce a wa'adin mulki.

An jima ana kai ruwa rana tsakanin 'yan adawa da bangaren masu mulki game da da zaben da ma yunkurin hana canza kundin tsarin mulki da kungiyoyyin rajin kare demukuradiyya suka sha yi, lamarin da ya hadasa mutuwar mutane da dama.