1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Ana tuhumar tsohon shugaban Ajantina da keta hakkin mace

August 15, 2024

Babban mai gabatar da kara na kasar Ajantina ya tuhumi tsohon shugaban kasar Alberto Fernández da laifin cin zarafin tsohuwar abokiyar zamansa Fabiola Yáñez da suka shafe shekaru goma tare.

https://p.dw.com/p/4jU0c
Tsohon shugaban kasar Ajantina Alberto Fernandez
Tsohon shugaban kasar Ajantina Alberto Fernandez Hoto: Johanna Geron/REUTERS

Babban mai gabatar da karar Ramiro González ya ce yana da shaidu da ke nuna cewar Shugaba Fernández ya aikata manya da kananan laifukan cin zarafi da suka hadar da duka da azabtarwa ga tsohuwar abokiyar zamansa, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AP ya samu daftarin hukuncin da kotun ta gabatar.

Karin bayani: Ajantina: Nasarar Alberto Fernandez

Kazalika mai gabatar da karar ya kuma bukaci tsohon mai kula da lafiyar shugaban kasa Federico Saavedra da kuma tsohuwar sakatariyar fadar shugaban kasar ta Ajantina María Cantero da su gurfana gaban kuliya domin bayar da bahasi.

Karin bayani: Alfarma ya jawo wa minista murabus a Ajantina

Sai dai Alberto Fernández da ya mulki kasar ta Ajantina daga shekara ta 2019 zuwa 2023 ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa tare da jaddada cewa zai kalubalanci wannan tuhuma a kotu.