1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

WTO na zama domin amincewa da nadin Okonjo-Iweala

February 15, 2021

Kungiyar Cinikayya ta Duniya, WTO, ta kira taro na musamman a wannan Litinin domin zaben shugabar kungiyar da ake kyautata zaton Tsohuwar Ministar Kudin Najeriya  Ngozi Okonjo-Iweala ce za a nada a wurin wannan zama. 

https://p.dw.com/p/3pMHJ
Schweiz Weltwirtschaftsforum in Davos Ngozi Okonjo-Iweala aus Nigeria
Hoto: dapd

Tun a watan Nuwamba aka yi tsammanin yin ittifakin bai wa Ngozi Okonjo-Iweala wannan kujera amma Tsohon Shugaban Amirka Donald Trump ya yi ta nuna turjiya kan yunkurin. Sai dai goyon bayan da a yanzu gwamnatin Amirka ta Joe Biden ta ba 'yar Najeriyar ya sanya jama'a gamsuwa cewa ita ce za a zaba a zaman na yau a matsayin 'yar Afirka kuma mace ta farko da za ta jagoranci WTO din. Ana sa ran  Ngozi Okonjo-Iweala ta yi jawabi jim kadan bayan an sanar da zaben nata a wannan matsayi mai muhimmanci.