1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hukumar Lafiya na son ganin an halasta ganyen wiwi

Suleiman Babayo RGB
December 8, 2020

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a rage takurar da ake yi kan ganyen wiwi saboda ana iya amfani da shi ta hanyar magani.

https://p.dw.com/p/3mPP6

A wani kudirin Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 1961 aka haramta amfani da wasu nau'in kwayoyi da ake gani masu hadari ne ga rayuwar dan adam. Wannan ya zama manufofin da ake aiki da su kan magunguna. A shekaru 60 da suka gabata ganyen wiwi yana daga cikin jerin haramtattun kwayoyi tare da hodar iblis. Amma yanzu an samu sauyi kan ganyen wiwi.

Wannan sauyi ya samu sakamakon kuri'ar da aka kada kuma aka samu rinjaye da kasashe. Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a rage takurin da ake yi kan ganyen wiwi saboda ana iya amfani da shi ta hanyar magani, kuma abin da aka amince a kai ke nan. A karkashin kudurin na shekarar 1961 an lissafa tabar wiwi sau biyu, kuma a jerin farko dama a nuna amfani da shi a matsayin magani.

Ana fatar ganin sakin mara daga gwamnatocin kasashe kan harkokin da suka shafi magani da ganyen wiwi, abin da ake gani ka iya rage tasirin kasuwar bayan-fage da ake sayar da ganyen na wiwi. Sai dai ga Alfedo Pascual mai rubuta sharhi kan abubuwan da suka shafi ganyen wiwi da tattalin arziki yana ganin zai yi wuya a ga wani sauyi kan sabon matakin na Majalisar Dinkin Duniya kan sake marawa batun na ganyen wiwi baya a domin magani.

Ya kara da cewa kasashen kamar Jamus da wasu na iya sassauta dokar hana amfani da tabar wiwi, amma duk da haka wasu musamman kasashe masu tasowa za su ci gaba da daukar wiwi a matsayin daya daga cikin abubuwa masu hadari, saboda rashin daidaito da za a samu kan matsayin gwamnatoci. Kamfanonin sarrafa magunguna za su ci gaba da duba irin tasirin kan sakin mara ga ganyen wiwi a bangaren kiwon lafiya.