1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana nuna wariya matuka a Amirka

Muntaqa AhiwaMarch 5, 2015

Rahoton bincike kan kisan wani matashi bakar fata a Ferguson na jihar Missouri ya tabbatar cewa jami'an tsaro na nuna wariya tsakanin farare da bakaken fatan Amirka,

https://p.dw.com/p/1ElDc
Protest & Ausschreitungen in Ferguson 29.11.2014
Hoto: Reuters/A.Latif

Babban mai shigar da kara na gwamnatin Amirka, Eric Holder, ya fitar da rahoton bincike kan kisar wani yaro bakar fata Michael Brown, da wani dan sanda farar fata ya harbe har lahira a Amirkar, cikin watannin da suka gabata. Rahoton dai ya ce ana nuna bambancin launin fata ga wadanda ke aikata irin wadannan kashe-kashe.

Sai dai wannan rahoton wanda ya wanke dan sandan da ya aikata kisan na Michael Brown, ya kai ga haddasa zanga-zanga. Inda 'yan sanda suka kame wasu mutane biyu a birinin na Ferguson da ke jihar Missouri. Masu zanga-zangar sun yi boren ne saboda wanke dan sandan da ya kashe matashin, wanda da rahoton na Holder ya yi.