Ana neman kawo karshen rikicin Mali | Labarai | DW | 16.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana neman kawo karshen rikicin Mali

Sassa Mali da ke fada da juna sun fara tattaunawar samar da zaman lafiya

Gwamnatin Mali da 'yan tawayen kasar sun fara tattaunawa a birnin Algiers na kasar Aljeriya da nufin samar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninsu. Kungiyoyi shida suka amince da shiga a damasu ciki kuwa har da MNLA da ke fafutukar samar da kasar abzunawa ta kashin kansu.

Wasu daga cikin kungiyoyin sun nemi a ba su kwarya-kwaryar cin gashin kai idan ana so su yi watsi da makamai. Ita ma dai gwamnatin Bamako ta nunar da cewar a shirye take ta dauki duk matakan da suka wajaba domin samar da zaman lafiya a arewacin kasar ta Mali.

Tun lokacin da Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ya dare kan kujerar mulkin Mali a watan Agustan 2013, batun tattaunawar zaman lafiya ke tafiyar hawainiya a arewacin kasar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Suleiman Babayo