1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mozambik: Ana murna da yarjejeniyar zaman lafiya

Gazali Abdou Tasawa MNA
August 7, 2019

A Mozambik tsohuwar kungiyar tawayen kasar ta Renamo wacce ta rikide zuwa jam'iyyar siyasa ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin Maputo shekaru 27 da kawo karshen yakin basasa na farko a kasar. 

https://p.dw.com/p/3NTnv
Mosambik Maputo | Filipe Nyusi und Ossufo Momade unterschreiben Friedensabkommen
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Shugaba Filipe Nyuzi da shugaban jam'iyyar ta Renamo Ossufo Monade sun saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar a birnin Maputo a gaban dubunnan jama'a da suka hada shugabannin kasashen Afirka kamar su Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu da Paul Kagame na Ruwanda. Ita ma dai kasar Jamus ta bakin Ministan Harkokin wajenta Heiko Maas ta yi maraba da yarjejeniyar zaman lafiyar da ta ce za ta bude sabuwar hanyar kawo karshen mummunan rikici a kasar. 

Wannan dai shi ne karo na uku da kungiyar ta Renamo da gwamnatin Maputo ke cimma yarjejeniyar zaman lafiya, amma kuma assalati ta warware daga baya inda Renamon ke kin mika makamanta a bisa zargin gwamnatin kasar da kin mutunta alkawurran da ta dauka. 

Wannan yarjejeniya da ake sa ran a wannan karo za ta dore na zuwa ne a lokacin da ya rage 'yan watanni a gudanar da zabuka gama-gari a kasar wadanda aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga watan Oktoba mai zuwa.