Ana gudanar da zaɓe a nahiyar Turai
May 25, 2014Talla
Al'umma a cikin ƙasashe 21 bisa 28 da suka yi saura na nahiyar Turai na jefa ƙuri'a a zaɓen majalisar dokokin Turai. Mutane kamar miliyam dubu 388 waɗanda suka cancanci yin zaɓen, za su kaɗa ƙuri'a domin zaɓen wakilan 'yan majalisu 751 na nahiyar, a cikin ƙasashen Girka da Jamus da Faransa da dai sauransu a wani wa'adin mulki na shekaru biyar.
Sannan kuma za a zaɓi shugaban ƙungiyar da kuma wanda zai jagoranci majalisar zartarwa na Kungiyar Gamayyar Turai.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe