Ana daf da kammala taron Doha | Labarai | DW | 07.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana daf da kammala taron Doha

Da alama har yanzu ana ci gaba da samun saɓanin ra'ayoyi tsakanin wakilai na ƙasashen duniya wajan cimma yarjejeniyar ƙarshe a taron sauyin yanayi na MDD

Ministocin kare muhali na duniya da masu sulhunta wa na ta ƙara ƙaimi ga taron sauyin yanayi na MDD dake gudana a birnin Doha na Qatar,domin ganin ƙasashen 193 da ke halartar taron sun cimma wata jarjejeniya, akan rage dumamar yanayi da za ta maye gurbin ta Kyoto wacce zata kammala a ƙarshen wannan shekara.

Rahotannin na cewar ana samun saɓannin ra'ayoyi tsakanin ƙasashen kudu da na arewa akan yin aiki da wani shashe na yarjejeniar ta Kyoto. na bayar da kuɗaɗen tallafi ga ƙasashen masu taso wa domin fuskantar lamarin na canyi yanayi.Ƙasashen Amurka da China waɗanda suka fi fitar da hayaƙi masana'antu mafi yawa a duniya suna addawa da shirin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Zainab Mohammed Abubakar