1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin zarafin Musulmi kabilar Uighur a Chaina

Zainab Mohammed Abubakar
September 18, 2018

Gwamnatin kasar Chaina ta dauki matakin takaita walwala da sa ido kan Musulmi tsiraru 'yan kabilar Uighur kimanin miliyan goma da ke zaune a gundumar Xinjiang da ke a Arewa maso yammacin kasar ta Chaina.

https://p.dw.com/p/356Yo
China Protest
Hoto: AP

Gundumar Xinjiang mai 'yancin kai da ke yankin Arewa maso yammacin kasar Chaina, gida ne ga al'ummar Musulmi na Uighur wajen miliyan goma. Sai dai gwamnatin China ta dauki matakai na takaita walwala ta hanyar sa ido kan Musulmin wannan yanki, da ma cafkesu ana kaisu wani sansani ana rufe su. 

Yining dai wani birni ne da ke gundumar Xinjiang da ke yankin Arewa maso yammaci. A hukumance ana kiran wannan gunduma mai 'yancin cin gashin kanta. Kuma mafi yawa daga cikin al'ummarta miliyan goma, Musulmi ne 'yan kabilar Uighur. Akilah mai shekaru 17 da haihuwa kuma Uiguren, tana aiki ne a matsayin Sabis a wannan wurin cin abinci , a cewarta lamura sun sauya sosai a birnin na Yining:

Ta ce " Mashigin kowane titi da ke garin nan akwai ofishin 'yan sanda. Kuma a kowace Litinin akwai inda ake taramu. Akalla mutane 500 ke hallara. Wajibi ne duk wanda ke wannan unguwa da kewaye ya halarci wannan zama".

Uiguren Proteste
Hoto: AP

Akan bayar da horo na musamman kan zama 'yan kasa na gari 'yan Uiguren. Jam'iyyar kwamunisanci ta Chaina ta haramta amfani da wasu alamu na Musulunci kamar taurari da makamantansu. Kazalika an haramta wa iyaye bai wa 'yan'yan da suka haifa sunan Musulunci. 

Domin tabbatar da hakan gwamnatin ta China na amfani da wani tsari na tura jami'anta tsakanin iyalai suna lura da yadda suke tafiyar da lamuransu, tare da tabbatar da cewar suna magana da harshen Sin, kuma haka lamarin yake a har a gidansu Akilah a Yining:

Ta ce "Suna lura da yadda muke rayuwa a kowace rana da abun da muke yi, da kuma irin matsaloli da muke fuskanta. Da farko dai babu wanda ya damu da hakan. Jami'an 'yan chainis ne, akan turo mutum guda ko kuma su biyu. Kuma a kowane wata za su kwana uku a gidanmu. Wani lokaci mazaje guda biyu, a wasu lokutan kuma namiji da mace. Namijin yakan kwana tare da mahaifina, kana macen ta kwana da mahaifiyata".

China Uiguren vor Execution 16.06.2014
Hoto: Reuters/CCTV

A 'yan shekarun da suka gabata dai gundumar Xinjiang ta fuskanci tarzoma da hare-haren ta'addanci.  Gwamnatin Chainar na zargin masu tsattsauran ra'ayi na Uiguren da hare-haren, kan haka ne ta mayar da hankali kan yaki da ayyukan tarzoma. Hakan ne kuma ya jagoranci ci gaban kutsawar da gwamnati ke yi cikin rayuwar Musulmin na Uighur.


Kungiyoyin kare hakkin jama'a sun shaidar da cewar, a yanzu haka akwai Musulmi sama da miliyan daya da ake tsare da su a wannan sansani na musamman, tun bayan kaddamar da wannan shiri na yakar ayyunkan tarzoma a wannan gunguma ta Xinjiang da ke yankin Arewa maso yammacin kasar ta Chaina.