Ana cikin zaman dar-dar a birnin Bangui | Siyasa | DW | 28.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana cikin zaman dar-dar a birnin Bangui

Mazauna kusa da kogin dake Bangui, babban birnin kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun fara tserewa daga birnin a cikin motoci da kananan kwale-kwale.

A daidai lokacin da dakarun 'yan tawaye suka ja daga a wani yanki dake kusa da Bangui babban birnin kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, suna jiran sakamakon tattaunawar da ake da nufin cimma shirin tsagaita wuta da gwamnati, mazauna kusa da kogin dake babban birnin sun fara tserewa a cikin motoci da kananan kwale-kwale, yayin da wasu suka fara jibge kayan abinci da ruwan sha.

Tun a ranar 10 ga watannan na Disamba kawancen 'yan tawayen SELEKA suka fara kutse a sassan kasar mai fama da talauci duk da dimbin arzikin ma'adanan karkashin kasa. Tawayen na wannan lokacin na zama wata barazana mafi girma ga mulkin kusan shekaru na 10 shugaba Francois Bozize da kuma ke barazanar janyo wani bala'i ga bil Adama. A wannan Juma'a an jiyo wani direban safa a tsakiyar Bangui babban birnin kasar ta jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na cewa damarsu ta karshe ita ce tattaunawa da 'yan tawaye.

Kokarin yin sulhu tsakanin 'yan tawaye da gwamnati

Zentralafrikanische Republik Präsident Francois Bozize bittet um Hilfe in Bangui

Shugaba Francois Bozize ya nemi taimako daga ketare

Yanzu haka dai jami'an dilomasiyya daga kasashen yankin tsakiyar Afirka suna a birnin na Bangui inda suke kokarin shimfida tubalin tattaunawa batun zaman lafiya da 'yan tawaye, yayin da ministocin harkokin wajen kasashen yankin ke wata ganawa a Gabon a kan rikicin. Gando Gilbert malami a jami'ar Bangui ya ce ana cikin zaman rashin sanin tabbas.

"A halin da ake ciki babu wanda ya san yadda wannan rikici zai ƙare. Wannan shine ke ƙara saka tsoro cikin zukatan jama'a. Sannan kuma akwai karancin labari, ko 'yan tawayen za su amince su hau teburin shawara ko kuma a'a. Ita dai ƙungiyar ƙasashen yankin tsakiyar Afrika ta yi wa ɓangarorin biyu tayin tattaunawa."

Kakakin kawancen kungiyar 'yan tawayen SELEKA, wadda ta lashi takobin kifar da shugaba Bozize face ya girmama yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma a baya da 'yan tawaye da ta tanadi biyan tsoffin mayaka kudade, ya ce za su dakatar da dannawar da suke yi zuwa Bangui domin ba da dama ga kokarin yin sulhu. Sai dai wata majiyar diplomasiya ta ce 'yan tawayen sun yi wa birnin kawanya.

Kasashen yamma sun yi biris da taimaka wa shugaba Bozize

A ranar Alhamis gwamnati ta yi kira ga kasashen Faransa da Amirka da su taimaka mata ta kori dakarun 'yan tawayen, amma gwamnati a Paris ta ce ba za ta yi amfani da sojojinta don kare gwamnatin Bozize ba yayin da Washington ta kwashe ma'aikatan ofishin jakadancinta dake birnin Bangui.

Soldat im Tschad

Sojan Chadi a cikin damara

Sai dai makociyar kasar wato Chadi ta aike da dakaru da za su mara wa na rundunar sojin Afirka ta Tsakiya, sai dai ba a sani ba ko za su iya tinkarar mayakan 'yan tawayen. Haroun Kabadi shugaban Majalisar dokokin Chadi ya karanta jawabin da shugaban ƙasa yayi game da batun aika sojoji a Jamhuriya Afrika ta Tsakiya:

"Shawarar farko da mu ka yanke ita ce mu tura tawagar sojoji a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya domin maido doka da oda. Wannan tawaga za ta ƙara ƙarfin karfin giwa ga rundunar sojojin ƙungiyar ƙasashen yankin tsakiyar Afrika. Mun ɗauki wannan ƙuduri daidai da dokokin ƙungiyar ƙasashen yankin tsakiyar Afrika da su ka umurci ko wace ƙasa memba ta kai ɗauki ga 'yar uwarta da ta fuskanci mamaya. Sojojin da muka tura za su yi aiki ƙarƙashin umurnin ƙungiyar ƙasashenmu."

A wani abin da ke zama an yi gudun gara an fada wa zago, mutane a cikin kwale-kwale na tserewa daga bangaren kogin Oubangui zuwa Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo dake daya bangaren.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin