Ana cigaba da Allah wadai da kisan baki a Afirka ta Kudu
April 18, 2015Talla
Kasashen duniya da kungiyoyi na kare hakkin bani Adama na cigaba da nuna takaicinsu dangane da yadda ake cigaba da kisan baki da washe dukiyarsu a wasu sassa na Afirka ta Kudu.
Wadanda wannan lamari ya shafa sun zargi mahukuntan kasar da gaza tabuka komai wajen kawo karshen kisan 'yan kasashen wajen a kasar duba da yadda wadanda ke aikata hakan ke cin karensu ba babbaka.
Wannan yanayi da ake ciki a kasar ya sanya wasu kasashen musamman ma na Afirka kwashe al'ummarsu daga kasar don gudun kada su fada tarkon masu kyamar bakin.
A wasu kasashen kuwa ciki har da Zimbabwe, mutane ne suka yi zanga-zanga ta nuna rashin amincewarsu da kisan na baki 'yan Afirka a kasar, inda suka bukaci kawo karshen batun cikin hanzari.