Ana ci gaba da zanga-zangar adawa da Shugaban Kwango | Labarai | DW | 21.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da zanga-zangar adawa da Shugaban Kwango

Rikicin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango na kara zafafa kan adawa da shirin shugaban kasar da ci gaba da mulki

An yi harbe-harbe lokacin da dalibai suke zanga-zanga da ta shiga kwana ta uku a Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango, domin nuna adawa da shirin Shugaba Joseph Kabila na kara wa'adin mulkinsa.

An harbi mutane biyu lokacin da masu zanga-zangar suka yi fito na fito daga jami'an tsaro kusa da jami'ar birnin. Shugaba Kabila ya kwashe shekaru 14 kan madafun ikon kasar, sannan wa'Adinsa zai kawo karshe a shekara mai zuwa ta 2016. Sai dai ana zargin Kabila da yunkurin neman ci gaba da zama kan madafun ikon kasar da ke yankin tsakiyar nahiyar Afirka. Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta ce mutane 42 suka mutu a rikicin, sannan wasu fiye da 100 suka samu raunika.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman